1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta wallafa bidiyon kisan mutane a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 27, 2019

Kungiyar IS mai fafutikar jihadi a yammacin Afirka (ISWAP) ta wallafa bidiyon da ke nuna irin yadda ta yi kisan wasu mabiya addinin Kirista 11 a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3VOPp
Boko Haram Flagge (S. Yas/AFP(Getty Images)
Hoto: S. Yas/AFP(Getty Images

Faifan bidiyon da aka wallafa a shafukan kungiyar na farfaganda Amaq ya nuna mutanen daukacinsu an rufe fuskokinsu, inda aka bindige na farko kan daga bisani a yayyanka naman sauran jama'ar da kungiyar ta yi garkuwa da su.

A gabanin yanka jama'ar daya daga cikin 'yan kungiyar ya gabatar da jawabinsa inda ya nuna kisan mutanen a matsayin wani sako ne ga mabiya addinin Kirista, kana kuma kisan na a matayin wata ramuwar gayya ce domin daukar fansan kisan jagoran kungiyar ta IS  Abou Bakr Al-Bagdhdadi, wanda sojojin Amirka suka yiwa dirar mikiya a cikin watan Oktoban da ya gabata a wata mabuyarsa da ke kasar Siriya.