1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta yi tir da harin Amurka a Iraki da Siriya

February 3, 2024

Gwamnatin Iran ta yi martani da kakkausan lafazi kan harin daukar fansar da Amurka ta kai a Iraki da Siriya, tana mai cewa Washigton ta taka dokar keta sararin samaniyar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4c0Yl
Harin fansar da Amurka ta kai Iraki
Harin fansar da Amurka ta kai Iraki Hoto: Hashd al-Shaabi Media Office/Anadolu/picture alliance

A cikin wata sanarwa mai magana da yawun hukumomin Teheran Nasser Kanani, ya ce samamen da Amurka ta kai babban kuskure ne da ka iya kara rura wutar tashin hankalin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya, sai dai ba yi karin haske ba kan ko an kashe wani sojan kasar a lokacin hare-haren.

Karain bayani: Amurka ta kai hare-haren daukar fansa a Iraki da Siriya 

A cewar wani sabon rahoto da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Siriya ta fitar ta ce harin na Amurka ya yi ajalin akalla mayaka 23 masu alaka da Iran, 10 a yankin Deir Ezzor sannan 13 a yankin Al-Mayadine.

Karin bayani: Amurka ta sha alwashin ramuwar gayya ga wadanda suka halaka sojojinta a Jordan

Samamen dai na daren Juma'a wayewar Asabar martani ne ga harin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Amurka uku a ranar Lahadin da ta gabata a wani sansani da ke Kudancin kasar Jordan a kan iyar Siriya, harin da Washigton ta dora alhakinsa ga gungiyoyi masu kaifin kishin Islama masu alaka da Iran.