1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta musanta zargin kisan sojojin Amurka

January 29, 2024

Iran ta musanta zargin cewa da hannunta a harin da aka kai da jirage marasa matuka wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Amurka uku a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4bmXh
Iran ta musanta zargin kisan sojojin Amurka
Iran ta musanta zargin kisan sojojin AmurkaHoto: REUTERS

Hukumomin Iran sun nisanta kansu daga zargin cewa da hannun kasar a hari da jiragi maras matuki wanda ya yi ajalin sojojin Amurka uku tare da jikkatar wadansu 30 a Arewa maso gabashin kasar Jordan. A cikin wata sanawa, kakakin ma'aikatar diflomasiyyar Iran Nasser Kanaani ya ce ana so a goga wa kasar kashin kaji ne domin cimma manufa ta siyasa da nufin kawar da hankula kan abin da ke faruwa a zahiri a yankin Gabas ta Tsakiya in ji shi. Wannan martani na Tehran ya biyo bayan wasu kalamai da jami'in diplomasiyyan Burtaniya David Cameron ya furta, inda ya yi kira ga Iran da ta guji rura rikicin da ake a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani: Amurka da Burtaniyya sun kai harin bama-bamai kasar Yemen kan 'yan tawayen Houthi

Jim kadan bayan harin na ranar Lahadi 28.01.2024, fadar shugaba Joe Biden ya zargi kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran, tare da yin barazanar daukar fansa kan masu tsattsauran ra'ayin Islama da suka aikata abin da ya sifanta da aika-aika.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kashe sojojin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.