1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta kai sabbin hare-hare kan Houthi a Yemen

January 18, 2024

Sojin Amurka sun kaddamar da wani sabon farmaki a kan makamai masu linzami da mayakan Houthi suka yi niyyar harbawa akalla 14 daga Yemen, a ci gaba da zafafa hare-haren da Amurkan ke kaiwa yankin a kasa da mako guda.

https://p.dw.com/p/4bOoW
Mayakan Houthi dauke da makamai a birnin Sanaa, Yemen
Mayakan Houthi dauke da makamai a birnin Sanaa, Yemen Hoto: Osamah Yahya/ZUMA Wire/IMAGO

Makaman masu linzami na mayakan Houthi da Amurkan ta lalata an shirya amfani da su ne wajen kai hari kan jiragen ruwan 'yan kasuwa da kuma na sojin ruwan Amurkan da ke shawagi a yankin, a cewar cibiyar bayar da umarnin aiwatar da farmaki na Amurkan a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.

A cewar sojin na Amurka harin zai dakile kaifin hare-haren da mayakan Houthi suka kaddamar kan jiragen ruwan da ke dakon kayan fatauci da kuma na kasa-da-kasa da ke zirga-zirga a Bahar Maliya da zirin Bab-el-Mandeb da kuma gabar tekun Aden.

Mayakan na Houthi sun kaddamar da hare-hare ne kan jiragen ruwa a watan Nuwambar bara domin nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinawa da ke Gaza a yakin Isra'ila da Hamas, kuma hakan ya haifar da tsaiko tare da gurgunta kasuwanci tsakanin kasashen Asiya da Turai da jiragen ruwansu ke bin yankin.