1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Hukumar Raya Arewa maso Yamma

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 24, 2024

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana fafutukar ganin gwamnatin Najeriya ta kafa Hukumar Bunkasa Yankin Arewa maso Yammacin kasar da matsalar rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki ta afakawa a 'yan shekarun nan.

https://p.dw.com/p/4ih8D
Najeriya | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu | Tsaro | Arewa maso Yamma | Matsaloli
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Kafa Hukumar Bunkasa Yankin Arewa maso Yammacin Najeriyar dai, muhimmin mataki ne a kokarin kai dauki da tallafa wa wannan yanki. Matakin dai ya sanya murna har baka ga daukacin al'ummar yankin da suka kunshi jihohi bakwai, wadanda suka hadar da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da Zamfara da Kebbi da kuma Sokoto. Majalisar dokokin Najeriya ce dai ta taka muhimiyya rawa a wanan fafutuka, domin can ne aka fara aza girkin da ya haifar da samuwar wannan hukuma. Sanata Barau Jibril shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya da ya gabatar da kudurin da ya zama dokar kafa hukumar, ya bayyana fatan cewa kamar yadda Hukumar Raya Yankin Niger Delta  da ke ayyukan gina hanyoyi da asibitoci da makarantu za a samu haka a yankin na Arewa maso Yammaci karkashin sabuwar hukumar. Kokarin bunkasa ci-gaban yankin da ke shan wahala musamman a fannin rashin tsaro na 'yan bindigar daji da suka mayara da shi cibiyarsu, abin da ya haifar da mumunan koma-baya ga al'ummarsa a fannin tsaro da tattalin arziki da ma yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Najeriya | Tsaro | Katsina | Zanga-Zanga
Al'ummar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, sun jima suna koke kan tsaroHoto: DW/H. Y. Jibiya

Yankin da a baya ke samar da dimbin kayan abinci ga Najeriya da ma kasashe makwabta musamman Jamhuriyar Nijar da Kamaru, a yanzu ya koma ana neman tallafin ciyar da alummarsa. Wannan ya sanya daukar matakin kafa hukumar, domin bin sahun irinta da aka kafa a yankin Niger Delta da ma Arewa maso Gabashin kasar. Kungiyoyin kasa da kasa sun sha jan hankali a kan kalubalen da ke fuskantar yankin musamman barazanar yunwa da yara kanana da ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki, saboda mumunan koma-bayan da ba a taba ganin irinsa ba a 'yan shekarun nan. Kungiyara agaji ta Likitocin na Gari na Kowa wato Doctors Without Borders ta ce a shekaru biyar da ta yi tana aiki a jihohi bakwai na yankin akwai abubuwa da ke daga hankali, abin da ya sanya dagewa wajen kafa hukumar. Alummar wannan yanki na fatan hukumar za ta kauce wa zargincusa siyasa wajen gudanar da ayyukanta, ta yi koyi da takwarorinta da aka samar a yankin Niger Delta da kuma na Arewa maso Gabas.