1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
FasahaAfirka

Samar da sana'a ga nakasassu

April 14, 2021

A kokarin janye samari matasa guragu daga barace-barace a kan hanya dan kama sana'ar yi, wani matashi nakasasshe ininiya a garin Kaduna na Najeriya ya horas da matasa nakasassu sana'ar walda.

https://p.dw.com/p/3s01k
Bildergalerie Die Welt spricht Sport Sambia
Hoto: Ralph Mouchbahani

Kimanin matasa mabarata guragu 70 ne, wanda wani matashin Kaduna injiniya wanda shi ma gurgun ne mai suna Isiyaku Musa Ma'ayi ya horas da ‘yan uwansa nakasassu sana'ar walda da kere-keren kofofin zamani da kekunan hawa da baburan nakasassu dan dogaro da sana'ar hannu maimakon yawo da kokan bara kan titunan Kaduna

Isiyaku ya kara da cewa akwai sana'o'i da dama da ya kamata suna yi, to amma akwai bukatar fargar da su mahinmancin koyan wani sana'a dan rufawa kansu asiri. Burin shi ne na ganin an rage yawan matasa da ke bara, saboda kama sana'ar hannu,

Ya ce akwai wurare masu yawa da suke horas da su, kuma daga ciki kullun suna samun karuwar yawan matasa guragu daga birane da karkara da ke zuwa koyan sana'ar walda dan yin ban-kwana da bara da ke damun hukumomi da sauran kungiyyoyin jama'a na Nijeriya

Daga cikin kalubalen da yake fuskanta akwai dai na rashin sayen kayan nakasassu da kuma rashin tallafi daga hukumomi da attajiran kasa dan karfafa masu wannan sana'ar. Wani matashin gurgu daga cikin wadanda ake horas da su ya nuna jin dadi bisa irin sauyin rayuwa da ya samu.