1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Matashiya mai sana'ar dinki

November 4, 2020

Binta Yusuf Mohammed matashiya ce 'yar kimanin shekara 23 a duniya, da ta rungumi sana'ar yin dinkin mata da maza da kuma kananan yara, bayan ta kammala karatunta na digiri.

https://p.dw.com/p/3ks1a
Nigeria Schneiderin in Kaduna
Matashiyar tela a Kaduna, Binta Yusuf MohammedHoto: Mohammed Mohammed/DW

Matashiya Binta Yusuf Mohammed dai, ta kammala karatun nata ne a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda a yanzu haka ta bude wani babban shago kuma tana da yara da suke gudanar da wannan sana'ar. Ta kuma bayyana cewa sana'ar dinki ta yi mata komai a rayuwa.

Binta Yusuf  ta ce tana shekarar karatu ta uku a jami'a ta fara sana'ar dinki, biyo bayan halayyar da ta ce teloli na yi mata. Matashiyar ta jajirce wajen ganin ta kafa kanta a wannan sana'ar, inda a halin yanzu ta bude shagon dinka kayayyaki na maza da mata da kuma kananan yara. Alo kuta da dama a kan koka da masu dinki musamman dangane da batun kammala aiki cikin lokaci.