1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Matashiya mai kanikanci

October 6, 2020

Wata matashiya a jihar Kaduna da ke Tarayyar Najeriya 'yar shekaru 22 da haihuwa, mai suna Sandra Dalladi Bah ta rungumi sana'ar gyaran mota wato kanikanci.

https://p.dw.com/p/3jVPW
Nigeria HdM: Kaduna Mechanikerin (F)
Matashiya mai sana'ar kanikanci a Kadunan NajeriyaHoto: Mohammed Mohammed/DW

Sandra Dalladi Bah matashiya ce 'yar kimanin shekaru 22 da haihuwa, a yanzu haka tana karatun diploma a fannin nazarin aikin jarida wato "Mass Communication" a kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna a Najeriya, ta bayyana cewa aikin kanikancin mota yai mata komai, domin har yanzu tana cin moriyarsa a matsayinta na diya mace.

Matashiyar ta ce ta fara sha'awar yin aikin kanikancin mota tun tana firamare, inda take ganin su da datti a koda yaushe. Hakan ya sa ta tambayi mahaifiyarta shin mahaukata ne? Amsar da ba ta samu ba ke nan sai da ta kara tasawa. Tun daga wannan lokaci Sandra ta dauki azama domin ganin ta cimma burinta a rayuwa wato yin aikin kanikanci, inda ta ce kwalliya na biya mata kudin sabulu. Ta kara da cewa tun daga karamar sakandire wannan aiki ke biya mata bukata har kawo yanzu da ta ke kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna.

Bayan rubuta jarrabawar tafiya gaba da sakandire, ta zauna babu kudin c igaba da karatu, sai ta mayar da hankali a kan wannan aikin. Kasancewar cewa babu inda ba a samun kalubale, matashiyar ta bayyana cewa kasa gano abin da ya samu mota da wuri na ci mata tuwo a kwarya, kuma tafi gyara kananan motoci. Sandra ta ce babban burinta a rayuwa, shi ne ta samu gareji mallakar kanta.