1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Himma dai Matasa: Matashi mai waina

September 29, 2021

Wani Matashi da ya kammala karatu babu aikin yi a jihar Katsina da ke Najeriya, ya kama sana'ar sayar da waina da naman kai domin dogaro da kai.

https://p.dw.com/p/412pd
Poffertjes mit puderzucker
Waina ko masa, sana'a ce da aka fi sanin mata na yiHoto: emmi - Fotolia.com

Matashin dai ya dauki matasa da dama aiki, suna masa tuyar wainar yana biyansu. Sana'ar dai ta zamarwa matasan sallar arziki. Matashin dai ya ce ya samu nasarori sosai, wanda hakan ne ya kara karfafa masa gwiwar rike sana'ar. Koda yake matashain ya ce, ba a rasa kalubale. Sana'ar toya waina kusan sana'a ce da aka fi sanin mata na yi a kasar Hausa. Matashin dai ya ce fatansa ya fadada wurin saida wainar, domin kara daukar wasu matasan aiki.