1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi mai gyaran Rim din mota

September 8, 2021

Wani matashi a jihar Kaduna da ke Najeriya, bayan kammala karatunsa ya kirkiri wani injin gyaran matattun rim din mota da ake sake anfani da su.

https://p.dw.com/p/403vg
Nigeria | Autofelgen in Kaduna
Musa Salisu Fanteka mai gyaran rim din mota a KadunaHoto: Ibrahima Yakubu/DW

Wani matashi a jihar Kaduna da ke Najeriya, bayan kammala karatunsa ya kirkiri wani injin gyaran matattun rim din mota da ake sake anfani da su. Matashin dai ya kammala karatunsa ne a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kadunan, sai dai kuma maimakon zaman jiran samun aikin gwamnati ko na kamfani matashin ya rungumi sana'ar sake sabunta tsofaffin rim din motocin. Matashin mai suna Musa Salisu Fanteka ya nunar da cewa, ya cimma manyan nasarori da wannan sana'a da ya runguma. Koda yake matashin ya ce akwai tarin kalubale, amma yana alfahari da sana'ar tasa da ke tallafawa rayuwarsa da ma ta sauran mutane da yake taimakawa.