1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kashe masu zuwa itace

June 23, 2023

Wani harin da ake kyautata zaton na 'yan Boko Haram ne ya kashe matasa da dama a wasu kauyuka Jere da Mafa na Jihar Borno da ke Arewa maso gabashinj Najeriya.

https://p.dw.com/p/4T0Gr
Taswirar Jihar Borno a arewacin Najeriya
Taswirar Jihar Borno a arewacin NajeriyaHoto: .

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun halaka matasa takwas ya yin da suke dawowa daji neman itace. Rahotanni sun ce matasan sun fito ne daga wasu yankuna hudu na kananan hukumomin Jere da Mafa da ke arewacin jihar Borno a Najeriya.

Sai dai mayakan sun kyale guda daga cikin matasan domin ya kai labari. Malam Zanna Aji Kaleri, guda daga cikin mahaifin matasan ya ya tabbatar da faruwar lamarin.

Tuni ma dai gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum wanda ya tabbatar da mutuwar wadannan Matasa ya yi ta'aziyya ga Iyalansu inda kuma ya ce za su dauki matakin tabbatar da tsaro a yankunan don manoma su samu damar yin noma.