1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin ta'addanci ya halaka jami'an gwamnatin Nijar da soja

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 3, 2024

Jami'an dai na kan hanyarsu ta zuwa Diffa da ke Kudu maso yammacin Nijar, inda maharan suka tsallako daga Najeriya suka harbe su

https://p.dw.com/p/4gZ5p
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Wani harin kwanton bauna ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an gwamnatin Jamhuriyar Nijar 3 da kuma soja guda daya da ke musu rakiya, a kan iyakarta da Najeriya, kamar yadda rundunar sojin Nijar din ta sanar.

Karin bayani:Nijar ta jaddada ci gaba da rufe iyakarta da Benin

Jami'an dai na kan hanyarsu ta zuwa Diffa da ke Kudu maso yammacin Nijar, inda maharan suka tsallako daga Najeriya suka harbe su.

Karin bayani:Nijar: Sojoji sun ki cewa komai kan dage takunkumin ECOWAS

Diffa da ke da iyaka da kasashen Kamaru da Chadi da kuma Najeriya, na fama da hare-haren 'yan Boko Haram tun a shekarar 2015.