1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harin Isra'ila ya hallaka fitaccen masanin kimiyya a Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 3, 2023

Kafin rasuwarsa, Sufyan Tayeh shi ne shugaban jami'ar Islama ta Gaza, kuma fitaccen mai bincike, kuma masanin kimiyyar Physics da lissafi a duniya

https://p.dw.com/p/4Zj0K
Hoto: Nutzung nur als Vorschaubild für den Beitrag

Wani harin sojin Isra'ila a Zirin Gaza ya hallaka fitaccen masanin kimiyya Bafalasdine Sufyan Tayeh da iyalansa, kamar yadda ma'aikatar ilimi mai zurfi ta yankin Falasdinu ta sanar.

Karin bayani:Amirka ta bai wa Isra'ila kyautar bama-bamai

Kafin rasuwarsa, Sufyan Tayeh shi ne shugaban jami'ar Islama ta Gaza, kuma fitaccen mai bincike, kuma fitaccen masanin kimiyyar Physics da lissafi a duniya.

A wani labarin kuma kasar Masar ta amince da karbar Falasdinawa sama da 600 masu dauke da Fasfo din kasashen waje, wadanda za su fice daga Zirin Gaza a Lahadin nan.

Karin bayani:Tattauna batun Gaza

Sama da 300 daga cikinsu dai Amurkawa ne da 'yan Canada gami da Jamusawa. Akwai ma wasu 'yan Norway da Girka da Turkawa da kuma 'yan kasar Philipines.