1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Taro kan Gaza

Suleiman Babayo AMA
November 29, 2023

Ministan harkokin wajen Iran ya yi zargin samun tsaiko kan takardun tafiyar tawagarsa zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya a Amirka.

https://p.dw.com/p/4ZaRf
Gaza | Zirin Gaza bayan fara tsagaita wuta
Zirin Gaza bayan fara tsagaita wutaHoto: Ibraheem Abu Mustafa/REUTERS

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya ce akwai yuwuwar zai rasa taro a helkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York game da Zirin Gaza a wannan Laraba saboda rashin samun takardun tafiya na Amirka a kan lokaci na wakilan kasar ta Iran. Ana sa ran ministan harkokin wajen na Iran ya kasance lokacin wannan tattaunawar na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Wannan tattaunawar tana zuwa lokacin da aka tsagaita wuta bisa dalilan jinkai, inda ake sakin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su daki-daki yayin da Isra'ila take sakin fursunoni Falasdinawa.

Shi dai Hossein Amir-Abdollahian ministan harkokin wajen Iran da kasarsa suna cikin masu goyon bayan tsagerun kungiyar Hamas na Falasdinu.

Haka na zuwa lokacin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya zargin Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila da dillace yankin Zirin Gaza na Falasdinu.