1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

'Yan Boko Haram sun zafafa hare-hare a Borno

July 27, 2018

Kura ta lafa inda jama'a suka fara komawa harkokin yau kullum bayan da aka shiga halin rudani sakamakon hare-haren da wasu ‘yan bindiga da ake zaton mayakan Boko Haram suka kai wasu sassan Jihar Borno da ke Najeriya.

https://p.dw.com/p/32DRq
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

An dai dau tsawon lokaci ana ba-ta-kashi tsakanin mayakan na Boko Haram da Sojoji gami da ‘yan Sanda kafin dakile harin kamar yadda rundunar Sojoji da ta ‘yan sanda su ka sanar a sakonnin da suka aikewa manema labarai.

Sai dai duk bangarorin jami'an tsaron da ba su ba da cikakken bayani kan yawan mutanen da harin ya rutsa da su ko suka mutu ko suka jikkata. Sai dai wasu da suka tsira daga harin sun bayyana cewa an halaka jami'an tsaro da kuma wasu fararen hula tare jikkata mutane  wanda yanzu haka suna samun kulawar likita a asibitin kwararru da ke Maiduguri.

Irin makamancin harin Boko Haram a baya
Hoto: Reuters

Mayakan na Boko Haram sun kuma kai wani harin a garin Gajiganna inda jami'an tsaro tare da taimakon jiragen yaki ta sama sun fattaki mayakan kafin su shiga sansanin sojojin da ke garin.

Yanzu haka kuma rundunar sojojin Najeriya ta yi garanbawul ga manyan hafsoshin da ke kula da yaki da Boko Haram inda aka sauya babban kwamandan rundunar da ke yaki da Boko Haram da ake kira Operation Lafiya Dole da kuma babban kwamandan rundunar hadin gwiwa da ke wanzar da zaman lafiya a bakin gabar Tafkin Chadi.