1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Isra'ila sun shafi filayen jiragen Siriya

October 12, 2023

Siriya ta ce, hare-hare ta sama da Isra'ila ta kaddamar din ya shafi filayen jiragen samanta na Damasucus da kuma Aleppo.

https://p.dw.com/p/4XSWr
Filin jirgin sama na Aleppo da ke Siriya
Filin jirgin sama na Aleppo da ke SiriyaHoto: Stringer/Xinhua/imago images

Kamfanin dillancin labaran kasar SANA ya ruwaito cewa, babu wanda ya rasa ransa a hare-haren. Kawo yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai dangane da lamarin ba. Harin na zuwa ne kwana guda bayan da ministan harkokin wajen Iran ya shirya kai ziyara kasar domin ganawa da hukumomi kan halin da yankin ke ciki.

Dama dai Isra'ila na kai hare-hare kan filayen jirgin sama da kuma tasoshin ruwan kan yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin Siriya a wani mataki na dakile shigar da makamai ga 'yan tawayen da ke samun goyon bayan gwamnatin Tehran, ciki har da 'yan kungiyar Hezbollah na Lebanon.