1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine: NATO na samun turjiyar Hangari

Binta Aliyu Zurmi LMJ
June 13, 2024

Amurka da sauran kasashen Yamma na fadi tashin samar wa kasar Ukraine karin tallafi na biliyoyin kudi, yayin da Ukraine da Rasha ke ci gaba da yakar juna.

https://p.dw.com/p/4h0bQ
 Jens Stoltenberg | NATO | Ukraine | Tallafi
Sakatare janar na kungiyar Tsaro ta NATO Jens StoltenbergHoto: Efrem Lukatsky/AP Photo/picture alliance

Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da kungiyar Kawancen Tsaron ta NATO ke dari-dari da kasar Hangari da ke mammaba a kungiyar kuma zama kawa daya tilo ga Rasha. Hangarin ta jima da nuna kin amincewarta da bai wa Ukraine tallafin makamai da sunan kungiyar, wanda a cewar mahukuntan Budapest hakan ka iya kai NATO da Rasha ga yaki. A yanzu haka ma, kungiyar na fuskantar turjiya daga firaminista Victor Orban. Sai dai bayan wata ziyara da sakatare janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya kai masa, sun cimma yarjejeniya a kan cewa kasar Hangari ba za ta hana ba kuma ba za a yi da ita ba. Wannan dai shi ne karon farko da kasashe mambobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, ke shirin aika makamai zuwa Ukraine da sunan kungiyar da ta jima tana kallon Rasha a matasayin wata barazana ga Turai.

Tallafi | NATO | Ukraine |  Yaki | Rasha
Ukraine ta jima tana samun tallafin Kasashen Yamma a yakin da take da RashaHoto: Amien Essif/DW

Kungiyar NATO dai ta sha alwashin sama da tallafin kimanin dalar Amurka biliyan 40 ga Ukraine a kowace shekara, har sai sanda yakinta da Rasha ya kawo karshe. To sai dai, tana kokarin yin kaffa-kaffa domin gudun fadawa yaki kai tsaye da Rashan. Masharhanta na ganin matakin da Hangari ta dauka ka iya zama cikas ga kungiyar ta NATO, kasancewar Firaminsta Orban ya jima yana kokarin samar da sulhu a tsakanin kungiyar da Rasha na cewar ba lallai ba ne a koda yaushe ra'ayi ya zamanto daya. A watan Yulin gobe ne kungiyar ta NATO za ta gudanar da babban taronta a kan sabbin hanyoyin da zasu fito da su na ci gaba da bai wa Ukraine tallafi, a daidai lokacin da take fargabar yiwuwar dawowar tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan madafun iko. Amurkan dai na zaman wadda ta fi bayar da kaso mai tsoka ta  fuskacin gudanar da kungiyar ta NATO, kuma ana hasashen dawowar Trump ka iya kawo cikas.