1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hamas ta harba rokoki zuwa Isra'ila

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 7, 2024

Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ce matukar duniya tana son zaman lafiya to wajibi ne ta mara ma ta baya.

https://p.dw.com/p/4lTdt
Hoto: Ariel Shalit/AP Photo/picture alliance

Kungiyar Hamas ta yi ikirarin harba rokoki zuwa kudancin Isra'ila a wannan Litinin, a daidai lokacin da ake cika shekara guda da harin da ta kai wa Isra'ila bara, wanda ya sabbaba yakin da ake ci gaba da gwabaza wa tsakanin bangarorin biyu.

Wata sanarwa da dakarun Ezzedine Al-Qassam suka fitar, ta ce sun kai hare-haren ne mashigin Rafah da Kerem Shalom, sai kibbutz Holit da ke kusa da iyakar Gaza.

Tuni dai rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kai harin, amma ta ce ta samu nasarar kakkabo uku daga cikinsu, mintuna kalilan da fara jimamin tuna wa da harin bara.

Karin bayani:Shekara guda da harin 7 ga watan Oktober a Isra'ila

A gefe guda kuma kungiyar iyalan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da 'yan uwansu ta sanar da mutuwar guda daga cikinsu da ke Gaza, kuma Hamas din ta ki bayar da gawarsa. 

Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ce matukar duniya tana son zaman lafiya to wajibi ne ta mara ma ta baya.

A wani labarin, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi sammacin jakadan Australia a Tehran Ian McConville, don ba da ba'asi kan matsayar da kasarsa ta dauka na karkatar da goyon bayanta ga Isra'ila, bayan harin ramuwar gayyar da ta Iran ta kai ma ta.

To sai dai wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Australia ta fitar ta nuna cewa tana nan kan bakanta na sukar harin da Iran ta kai wa Isra'ila, kuma ba ta yi da na sanin daukar matakin ba.

Karin bayani:Rikicin Israila da Hizbullah: Mene ne sirrin kemewar Iran

A Talatar makon da ya gabata ne Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kusan 200 kan Isra'ila, a matsayin ramuwar gayyar kisan da dakarun sojin Isra'ila suka yi wa shugaban kungiyar Hizbullah ta Lebanon Hassan Nasrallah.

Isra'ila ta sha alwashin mayar da zazzafan martani kan abin da ta kira gagarumin kuskuren da Iran ta tafka.