1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hamas ta dakatar da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

July 14, 2024

Kungiyar Hamas ta ce ya yanke shawarar dakatar da duk wata tattaunawar tsagaita wuta a zirin Gaza, kwana guda bayan harin da Isra'ila ta kai wa wani shugabanta.

https://p.dw.com/p/4iGjD
Gazastreifen | Angriff auf ein Zeltlager in Khan Younis
Hoto: Mohammed Salem/REUTERS

Wani jigo a Hamas ya sanar da cewa kungiyar ta daukin matakin dakatar da duk wata tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza soboda kisan Falasdinawa 92 da Isra'ila ta yi a ranar Asabar a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Mawasi da ke kudancin Gaza a tsakanin birnin Rafah da Khan Younous.

Karin bayani: Za a koma teburin neman tsagaita wuta a Gaza

Sai dai Isra'ila ta musanta kisan fararen hular da ake zarginta da aikata wa inda ta ce dukannin wadanda ta hallaka 'yan ta'adda ne na kungiyar Hamas da suka killace gurin da ta kai harin.

Karin bayani: Isra'ila ta yi na'am da shiga tattaunawa da Hamas

A daya bangare kuma Hamas ta ce babban jami'in sojinta Mohammed Deif da Isra'ila ke ikirarin halakawa na nan a raye, kuma yana ci gaba da jagorantar ayyukan rundunarta ta Al-Qassam.