1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darasin rayuwa: Hadarin ababen hawa fitina ga rayuwa

Abdoulaye Mamane Amadou AH
August 11, 2023

Akalla mutane miliyan daya da rabi ne ke mutuwa a duk shekara samakon hadurran ababen hawan da ake samu a sassan duniya. Wasu miliyan 20 zuwa 50 na samun munanan raunukan da suka hada da rasa wani bangare na jikinsu.

https://p.dw.com/p/4V2Kd
Türkei Erzurum | Meral Danis Bestas - HDP Politikerin bei Verkehrsunfall verletzt
Hoto: DHA

Wannan lamarin na hadasa mummunan illa ga rayukan wadanda Allah ya tarfa wa garinsu nono da kasancewa suna da raguwar numfashi a duniya. Duk da yake babu wasu cikakkun alkaluman da suka bayyana a zahiri wadanda suka jikkata sakamakon hadduran a Najeriya kawai matsalar ta kashe mutane  fiye da dubu tara da rabi a bara baya ga wasu dubban da suka jikkata.

Hadurran ababnen zirga-zirga na zama sanadin rasa wani bangare na sassan jiki

Kenia I Verkehrsunfall in Londiani
Hoto: John Njoroge/AP/picture alliance

A jamhuriyar Nijar rayukan mutuane fiye da 1200 ne suka salwanta ta hanyar hadurran na ababen hawa a shekara ta 2021, wannan ya sa kasar ta kasance ta bakwai a wannan lokaci daga cikin jerin kasashen Ecowas masu fama da hadurran ababen hawa a yammacin nahiyar Afirka.