1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hadarin mota a Masar ya hallaka gomman mutane

Binta Aliyu Zurmi
October 5, 2024

Rahotanni daga kasar Masar na cewar hadarin wata motar dakon fasinja ya yi sanadiyar rayukan mutane 8 tare kuma da jikkata wasu mutane sama da 10.

https://p.dw.com/p/4lReo
Äthiopien Autounfall in Mareko
Hoto: Mareko special district government communication office

Hadarin wanda rahotanni suka ruwaito motar ta kwace daga hannu direba kafin daga bisani ta kuma fada a dayan hannu da motoci ke tafiya ya auku ne sakamakon gudu mara kima da direban ke yi.

Kasar masar kamar wasu kasashen Afrika na fama da yawaitar hadarin mota akai-akai wanda ake alakanta shi da rashin kyawun hanya da ma rashin kula daga bangaren dirobobin.

Shekara guda ke nan a watan Oktoban bara wasu motoci makare da fasinjoji suka yi taho mu gama a wata babbar hanya da ke Cairo lamarin da nan take ya hallaka mutane sama da 30.

Karin Bayani: Hadarin mota fitina ga rayuwar dan Adam