1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ghana ta kaddamar da aikin gina matatar man fetir

August 20, 2024

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya kaddamar da aikin gina matatar man fetir da za a kashe dalar Amurka biliyan 12, tare da fitar da gangar mai lita dubu 300 a kowacce rana, matakin da shugaban ya ce abin farin ciki ne.

https://p.dw.com/p/4jhso
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-AddoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS

Ghana da ke kasancewa kasa ta biyu da ke da arzikin koko a duniya, ta shiga cikin jerin kasashen da ke karfin arzikin man fetir ne a 2020. Alkaluma sun nuna cewa kasar na fitar da gangar mai 132,000 a kullum tare da makamashin iskar gas mai yawan gaske.

Karin bayani:Ghana ta samu ci gaba ta fuskar arzikin zinare 

Matatar man fetir din za ta kasance guda daga cikin ayyukan da za su bunkasa tattalin aryikin kasar, a cewar shugaba Akufo-Addo, a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da shirin a yankin Jomoro da ke kudu masu yammacin kasar.

Karin bayani:  Asusun IMF ya sake bai wa Ghana rancen Dala miliyan 360

A wata kididdiga da kungiyar sarrafa albarkatun mai ta nahiyar Afirka ta fitar, ta ce kasashen Afirka ta Yamma na amfani da gangar man fetir 800,000 a kowace rana, wanda kashi 90% bisa 100 daga waje ake shigo da shi.