1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Gaskiyar Magana: Ceto darajar naira a Najeriya

February 23, 2024

https://p.dw.com/p/4cnvD

A shirin na wannan makon mun tabka muhawara a kan yadda za a ceto darajar naira daga durkushewar da ta ke yi, lamarin da ke jefa al'ummar Najeriya a cikin wani mawuyacin hali. Mun tattauna da Farfesa Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin kasa a Najeriya da kuma Muhammad Almustapha Naira, mataimakin mai kula da dokokin kungiyar 'yan chanji ta Abuja, babban birnin Najeriya.