1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

'Yan Isra'ila na neman Netanyahu ya yi marabus

Abdourahamane Hassane
June 18, 2024

Dubban ‘yan Isra'ila sun gudanar da zanga-zanga domin neman a gudanar da zabe kafin wa'adi

https://p.dw.com/p/4hB9M
Hoto: Ohad Zwigenberg/AP Photo/picture alliance

' Yan adawar na sukar firaminista Benjamin Netanyahu kan yadda yake tafiyar da yakin Gaza da kuma gazawarsa wajen kubtar da mutanen da Hamas ke yin garkuwa da su. A halin da ake ciki a yankin Falasdinu, shaidu sun ba da rahoton harin da Isra'ila ta kai, cikin dare, bayan dakatar da hare-haren a kudancin   Gaza saboda ayyukan jin kai.