1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 11 a Gaza

June 16, 2024

Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun tsagaita wuta na dan lokaci a wannan Lahadi a kudancin zirin Gaza da nufin ba da damar kara yawan kayan agaji da ake shigar wa yankin na Falasdinu da yaki ya jefa cikin bala'i.

https://p.dw.com/p/4h63N
Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon 'yan sa'o'i a Gaza
Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon 'yan sa'o'i a GazaHoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

A cikin sanarwar da suka fidda sojojin na Isra'ila sun ce za a dakatar da yaki daga takwas na safiya zuwa karfe bakwai na maraicen Lahadin nan a mashigin Kerem Shalom da kudancin Gaza zuwa mararrabar hanya ta Salahaddine.

Kazalika Isra'ilar ta sanar da mutuwar sojojinta 11 a yayin gumurzu da kuma fashewar wasu abubuwa a ranar Asabar a zirin na Gaza inda yaki ke daukar dumi yau sama da watanni takwas. 

Karin bayani: Amirka na kokarin an cimma shirin tsagaita wuta a Gaza

Wannan mataki dai ya biyo bayan tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya da kuma wasu kungiyoyin na kasa da kasa suka yi da mahukuntan Isra'ila kan samun karin kayan agaji da za su shiga yanki Falasdinu da ke fama da barazanar yunwa.

Karin bayani: Musulmi na gudanar da babbar Sallah ta 2024

A daya gefe kuma matakin zai bai wa al'ummar Gaza dama domin sararawa musamman a daidai wannan lokaci da ake bukukuwan babbar Sallah.