1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gallant: "Mun kashe ko jikkata fiye da rabin mayakan Hamas"

Mouhamadou Awal Balarabe
July 10, 2024

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya bayyana cewar sojojin kasarsa sun yi nasarar kashe ko kuma jikkata kashi 60% na mayakan Hamas, bayan da suka shafe watanni tara suna yaki da kungiyar ta yankin Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4i73f
Ministan tsrain Isra'ila Joav Galant
Ministan tsrain Isra'ila Joav GalantHoto: DREW ANGERER/AFP/Getty Images

A Lokcin da yake jawabi a zauren majalisar dokokin Isra'ila ta Knesset, Yoav  Gallant ya yaba abin da ya danganta da nasarori masu yawa da rundunar kasar ta samu a kan Hamas, a daidai lokacin da rikicin ya shiga wata na goma duk da kokarin shiga tsakani da kasashen duniya ke yi don a tsagaita bude wuta. Sojojin na Isr'ila dai na ninka hare-hare a sassa da dama na Zirin Gaza tare da karfafa farmaki a tsakiyar birnin a kwanakin baya bayan nan.

Karin bayaniZa a koma teburin neman tsagaita wuta a Gaza

Sai dai zahirin abin da ke faruwa ya yi hannun riga da bayanin da gwamnatin Isra'Ila ta yi a farkon watan Janairun 2024, inda ta sanar da cewa ta kammala rusa duk cibiyoyin soji na kungiyar Hamas. Wata majiya da ke da kusanci da masu shiga tsakniya ta nuna cewar shugabannin hukumar leken asiri ta CIA da na Isra'ila na kan hanyar zuwa birnin Doha domin tattaunawa batun tsagaita bude wuta da Hamas da aka kasa cimma matsaya a kai.