1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bankado cin hanci na tsoffin shugabannin Najeriya

Uwais Abubakar Idris
September 23, 2020

A Najeriya, ana martani kan binciken FinCEN na bankado cin hancin miliyoyin daloli a asusun kasashen waje mallakar wasu tsoffin shugabanin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3iuJG
Kombobild  Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan und Atiku Abubakar

Wannan dai ba yanayi ne mai dadi ba ga wadanan jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriyar saboda makuddan kudadde ne na milyoyin daloli da kungiyar ke zargi na haramun ne da aka zuba a asusun jiya na tsofafin shugabanin Najeriyar da suka hada da Cif Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da ake zargi na badakalar nan ce ta rijiyar man Najeriyar Malabu 245 da har yanzu ake takadama a kanta.

Haka nan wannan kungiya ta kasa da kasa da ke aiki da kungiyoyi sama da 40 da suka hada da cibiyar binciken aikin jarida ta Premium Times da ma CISLAC ta ce tana sa ido a kai da kuma na kudadden a asusun tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da iyalansa wadanda suka kai dala trillion biyu. Mallam Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar CISLAC ya ce suna kallon lamarin a matsayin yunkuri na kara toshe ayyukan cin hanci da rashawa.

Tuni dai tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ya mayar da martani da cewa babu wanda ke sa ido a kan kudaddensa, kuma duka wannan batu ne na siyasa don an fitar da rahoton na FinCEN ne ‘yan saoi’ bayan da jamiyyarsa ta PDP ta lashe zaben jihar Edo. Amma ga Injiniya Buba Galadima jigo a jamiyyar PDP na jam'iyyar yace ko da kurari aka yi zai yi tasiri bisa abinda suka gani a ‘yan kwanakin nan.

Duk da cewa a lokutan baya Najeriya kan gaza hukunta mutanen da ake wa kalon shafaffu ne dai mai ko da kasashen Turai sun nuna masu ‘yar yatsa, amma kidan da ke canzawa na zama dole kanwar naki na rawa ya canza a kan wadanda ake zargi da rub da ciki da dukiyar kasa a Najeriyar, cike da fata ta samun sauyi a yanayi na kifi na ganinka mai jar koma