1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan al'umma bayan samun mai a Bauchi da Gombe

November 22, 2022

Shugabannin al’umma da mazauna jihohin Bauchi da Gombe sun nemi a samar mu su da aikin yi da kuma tsabtatacen muhalli daidai lokacin da aka kaddamar da aikin hakar danyen mai a jihohin.

https://p.dw.com/p/4Jtzg
Symbolbild I Russisches Gasfeld
Hoto: Alexander Nemenov/AFP/Getty Images

Bayan sanar da batun fara hakar mai a yankin arewa maso gabashin Najeriya, mazauna yankin sun fara yin kira ga hukumomi kan su mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi musamman ga matasa da kuma karuwar kamfanonin da za su zuba hannayen jari a yankuna wanda a baya-bayan nan kididdiga ta nuna cewa suna cikin wadanda ke fama talauci a kasar.

Nigeria Jugend Ingenieur Maiduguri
Matasan Bauchi da Gombe na fatan rabauta da aikin yi bayan fara hakar mai a jihohinsuHoto: Al Amin Muhammad/DW

Malam Abdullahi Adamu Zabo wani dan asalin yankin da aka samu rijiyoyin man kuma a zantawarsa da DW ya ce suna son ganin lamura a yankin sun daidaita sannan matasansun samu aikin yi inda ya kara da cewa ''aikin yi zai kara darajar yankin sannan kuma za a samu raguwar aikata laifuka tsakanin matasa.''   

Masu rajin kare muhalli a nasu bangaren sun nemi kamfanonin da za su yi aikin hakar su tabbata sun dauki matakai na alkinta muhalli domin magance irin abubuwan da su ka faru da gurbacewar muhalli a yankin da ake hakar mai a yankin Niger Delta da ke kudancin Najeriya.

Flash-Galerie Nigeria Öl 50 Jahre Ölförderung im Nigerdelta
Mazauna Gombe da Bauchi na fatan kada a samu gurbatar muhalli yayin aikin hakar mai a yankinHoto: AP

Su kuwa masana da masharhanta sun fi mayar da hankali ne kan yadda gwamnatocin jihohin za su samu abin da za su bunkasa jihohin da kuma inganta rayuwar al’ummar jihohinsu kamar yadda Dakta Umar Adamu da ke fashin baki kan harkokin yau da kullum a Najeriya ya nunar inda ya ce ''in har an samu gwamnatoci da kuma shugabannin masu amana ana da kyakyawan zaton cewa rayuwar al’umma za ta inganta sosai.''

Sai dai babban fatan da ake yi shi ne kada samun wannan albarkatun man ya haifar da rashin jituwa tsakanin jihohin da kuma samun gurbata muhalli a yankin kamar yadda aka gani a wasu jihohin da ke da albarkatun man fetur a Najeriya.