1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rashin tabbas na kara girma a zukatan jama'a

Usman Shehu Usman AMA(ZMA)
August 5, 2022

Batun tabarbarewar tsaro da fargabar kai hare-hare a Najeriya da wasu kasashen Afirka sun mamaye jaridun Jamus a sharhukansu da suka rubuta a wannan mako.

https://p.dw.com/p/4FBH1
Nigeria | Hari a gidan yarin Kuje na Abuja
Nigeria | Hari a gidan yarin Kuje na Abuja Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Tsoro ya cika babban birnin tarayyar Najeriya da wannan labarin ne jaridar die tageszeitung. Jaridar ta ce yayin da ake samu munanan hare-haren kungiyar Boko Haram a kewayen Abuja, rashin tabbas na kara girma a zukatan jama'a, an rufe makarantu a Abuja babban birnin Najeriya da kuma jihar Nasarawa mai makwabtaka.

A makon da ya gabata hukumar raya birnin tarayya Abuja ta bukaci duk wasu kamfanoni masu zaman kansu da su yi hakan saboda alamu na yiwuwar hare-haren kungiyoyin Boko Haram da ISWAP, ko baya ga Abuja da akwai kuma maganar tashar jiragen ruwa ta Legas, birni mafi girma a Afirka, inda 'yan sandan da ke wurin suka yi kira da a dau matakan tsaro mafi girma tare da yin kira ga daukacin mazauna yankin da su kara yin taka-tsantsan.

Barazanar kungiyar Alqa'ida ta koma sassan Afirka

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce kungiyar Al Qaeda ba ta taba bacewa ba inda ya a yanzu hatsarin ya koma ne daga rassan kungiyar a Afirka. Harin ban mamaki na karshe da aka danganta ga al-Qaeda ya faru ne makonni biyu kacal da suka wuce. Inda kimanin mayaka 500 daga kungiyar ta'addanci ta Somaliya Al-Shabab suka mamaye wani bangaren kasar Habasha, Sun toshe hanyar sadarwar a kudu maso yammacin Somalya, sun far wa garuruwa biyu da ke kan iyakarsu da Habasha. An yi fafatawa mai tsanani tsakaninsu da sojan Habasha. 

Takon saka tsakanin Mali da kasashen yammacin duniya

Sojojin Jamus sun ja daga a daya daga cikin sansanoninsu na kasar Mali
Sojojin Jamus sun ja daga a daya daga cikin sansanoninsu na kasar Mali Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Jaridar die tageszeitung  ta ce a sabon labari daga kasar Mali, shi ne ta rufe sansanin soja mafi girma na Majalisar Dinkin Duniya a Bamako babban birnin kasar. Dakarun Majalisar Dinkin Duniya wanda kasar Jamus ke da karfin fada aji cikinta, ayyukansu na kara tabarbarewa. Don haka ma jaridar ta ce a yanzu fa rayuwar dakarun Jamus a Mali na kara zama cikin rashin jin dadi, manufar da sojojin da ke mulki ke da ita shi ne na yi wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya wato Minusma wani kallo da tunani.  Sun hana motocin tawagar Majalisar Dinkin Duniya ke wucewa domin daukar sojojin kasashen waje a sansanin sojoji na Senou da ke filin tashi da saukar jiragen sama na Bamako.

Hakan ya fito ne daga wata wasika daga hukumar kula da tashar jiragen sama zuwa kamfanin Sahel Aviation Services (SAS), wanda ke gudanar da sansanin. An bukaci kamfanin na SAS a cikin wasikar da aka aika masa a ta "shirya janye sojojin kasashen waje daga harabarta" cikin sa'o'i 72 ´daga  ranar 2 ga watan Agusta.

Ko Afirka za ta ci moriyar dumbin makamashinta?

Mitar auna makamashin iskar Gas da ke karanci a Turai
Mitar auna makamashin iskar Gas da ke karanci a TuraiHoto: Thomas Trutschel/photothek/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung kuwa cewa ta yi. Ku cika takunan motocinku daga Afirka,  Saboda rashin iskar gas na Rasha, Jamus na son shigo da shi daga kasar Senegal. Baya ga Senegal ma dai a yanzu haka wasu kasashen Afirka suna shirin samarwa Turai albarkatun makamashi. Wannan ya haifar da damuwa tsakanin masu kare muhalli. Sabon yanayin da ake ciki a kasuwar iskar gas ta kasa da kasa yana nufin cewa mutane da yawa a Afirka sun fahimci wata da damar a rayuwa. A karshen watan Yuni, ministan man fetur da makamashi na kasar Mauritaniya ya bayyana a taron makamashi na Afirka da aka yi a Brussels cewa, hauhawar farashin iskar gas zai ba wa kasarsa da makwabciyarta Senegal da sauran kasashen nahiyar damar fitar da iskar gas zuwa kasashen waje. zuwa Turai. Kuma bai kamata Afirka ta bar wannan damar ya wuce ta ba.