1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki

July 7, 2024

Faransawa za su kada kuru'u a zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokokin kasar da ake ganin jam'iyyar masu kyamar baki ta iya samun nasara.

https://p.dw.com/p/4hyYz
Zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki a Faransa
Zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki a FaransaHoto: Artur Widak/picture alliance/NurPhoto

A wannan Lahadin Faransawa ke kada kuru'u a zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokokin kasar wanda ake ganin zai iya samar da gwamnatin masu ra'ayin rikau tun bayan yakin duniya na biyu.

Karin bayani: Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Faransa

Ana dai ganin ta yiwu jami'iyar masu kyamar baki ta Marine Le Pen, ta iya samun rinjaye a majalisar a karon farko. Idan har jam'iyyar ta National Rally ta lashe kujeru 289, ana sa ran Shugaba Emmanuel Macron ya nada shugaban jam'iyyar a matsayin sabon Firanministan kasar. Sai dai kuma babu tabbaci kan yadda sakamakon zai kasance saboda tsarin zaben da kuma yadda dukannin jam'iyyun suka dau damara.