1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Faransa

June 30, 2024

'Yan kasar Faransa zabe a zagayen farko na majalisar dokoki, zaben da Shugaba Emmanuel Macron ke neman samun rinjaye hajaran-majaran a cikin sa.

https://p.dw.com/p/4hh2N
Yadda ake zaben kasa a Faransa
Yadda ake zaben kasa a FaransaHoto: LUDOVIC MARIN/AFP

Da safiyar wannan Lahadi ne aka bude rumfunan zabe, inda mutum miliyan 49.3 da aka yi wa rajista za su zabi 'yan takara da suke muradi.

Bayanai na cewa kashi 25.9% na mutane sun fito kafin karfe 12 na rana agogon kasar, adadin kuma da ya zarta na zaben da aka yi shekaru biyun da suka gabata a daidai wannan lokacin da kashi 7.5%

Tun a jiya Asabar ne dai 'yan Faransar wadanda ke a kasashen ketare suka kada tasu kuri'ar saboda bambancin lokaci.

Ana kuma sa ran soma samun shigowar bayanan wadanda suka yi nasara jim kadan bayan karfe takwas na yammacin yau Lahadi.

Shugaban Faransar Emmanuel Macron ya kira zaben gaggawa ne dai, bayan gagarumar nasarar da jam'iyyar masu tsaurin ra'ayi ta Marine Le Pen ta samu a lokacin zaben majalisar Turai a farkon wannan wata.