1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta tabbatar da rufe ofishin jakadancinta a Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
January 2, 2024

Cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Paris, ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce watanni biyar ofishin jakadancinta a birnin Niamey ya shafe yana fuskantar cikas, lamarin da ya hana shi rawar gaban hantsi.

https://p.dw.com/p/4aoD0
Ofishin jakadancin Faransa a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar
Ofishin jakadancin Faransa a birnin Niamey na Jamhuriyar NijarHoto: AFP

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta jaddada cewa ta rufe ofishin jakadancinta da ke Nijar a hukumance jim kadan kafin Kirsimeti har sai abin da hali ya yi, amma za ta ci gaba da sauke wannan nauyi na diflomasiyya daga birnin Paris. Cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce watanni biyar ofishin jakadancin Faransa ya shafe yana fuskantar cikas a Niamey, lamarin da ke hana shi gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Karin bayani: Nijar: Ko alaka da Faransa ta zo karshe?

Ba kasafai ne kasashe ke yanke shawarar rufe ofishin jakadancinsu ba, amma wannan mataki na Faransa ya zo ne a daidai lokacin da rukunin karshe na sojojinta da ta jibje a Jamhuriyar Nijar da sunan yaki da ta'addanci suka bar kasar a ranar 22 ga watan Disamba.

Karin bayani:Jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar 

Paris da Niamey na fuskantar tsamin dangantaka tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin bara wanda ya hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum. Baya ma ga bukatar sojojin Faransa kusan 1,500 da si fice daga kasar, gwamnatin sojan Nijar ta kuma kori jakadan Faransa Sylvain Itté a karshen watan Agusta.