1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar

Salissou Boukari
September 27, 2023

Jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar bayan da a karshe shugaba Emmanuel Macron ya amince da janye jakadan.

https://p.dw.com/p/4WsnV
Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel MacronHoto: Geoffroy van der Hasselt/AFP

Tun dai a ranar 25 ga watan Augusta sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka bai wa jakadan Faransa wa'adin kwanaki biyu ya fice daga kasar sai dai shugaban na Faransa ya ce hakan ba za ta sabu ba domin bai yarda da sabbin hukumomin na Nijar a matsayin halastattu shugabanni ba. Sai dai kuma bayan kimanin wata guda da sanya kafar wondo daya tsakanin hukumomin na Nijar da na Faransa, a karshe shugaban na Faransa ya amince da janye jakadan da ma sojojin Faransa da ke jibge a kasar Nijar.

Dubban 'yan Nijar na nuna goyon baya ga sojoji da suka yi juyin mulki
Dubban 'yan Nijar na nuna goyon baya ga sojoji da suka yi juyin mulkiHoto: AFP/Getty Images

Tuni dai mutane da dama suka jima su na jan hankalin yan Nijar musamman wadanda ke da kishin ganin kasar ta samu cikakken mulkin kai daga turawan mulkin mallaka irin Faransa, inda suke cewa ko da ma jakadan ya tafi da ma sojojin dole sai an buda idanu ko'ina, kamar yadda Soumaila Amadou wani dan siyasa ya yi tsokaci.

Karin Bayani: Sabuwar baraka tsakanin Nijar da Faransa

Sai dai da yake magana kan wannan batu, Malam Nassirou Seidou shugaban kungiyar Muryar talaka, kuma mai sharhi kan harkokin siyasar duniya ya ce kasar Nijar dole za ta yi hulda da dukannin kasashe amma hulda ta mutunci da girmamawa:

Magoya bayan sojoji sun yi dandazo a kofar sansanin sojin Faransa
Magoya bayan sojoji sun yi dandazo a kofar sansanin sojin FaransaHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Ya zuwa yanzu dai masu fafutuka a Nijar sun ce suna ci gaba da samun kwarin gwiwa na kokuwar da suke yi wadda sannu a hankali ta ke samun sakamako ba tare da wani tashin hankali ba wanda a halin yanzu ma aka samu halartar yan fafutuka na Afirka da suka zo kasar ta Nijar daga sassa daban-daban domin kama wa Nijar din a kokuwar da take yi ta neman samun cikakken 'yanci da komawa cikakken tafarki na mulki cikin adalci wanda zai amfani yan kasa.