1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Faransa ta haramta sayar da ruwan roba mai guba na Olympics

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 20, 2024

Hukumar kula da ingancin abinci ta Faransa ta ce sinadarin Bisphenol A da aka yi robar na da illa ga kwayoyin halittar bil'adama da ke haddasa cutar sankarar mama

https://p.dw.com/p/4iXSx
Hoto: Tasos Katopodis/Getty Images

Faransa ta ba da umarnin janye wani ruwan sha na roba na kananan yara daga kasuwannin kasar, wanda aka yi shi na musamman don gasar Olympics, da za a gudanar a birnin Paris, sakamakon samun sinadari mai guba a mazubin.

karin bayani:'Yan damben wrestling na Rasha za su kauracewa Olympics na bana

Hukumar kula da ingancin abinci ta kasar ta ce sinadarin Bisphenol A da aka yi robar na da illa ga kwayoyin halittar bil'adama, da ke haddasa cututtuka, ciki har da sankarar mama.

Karin bayani:Nijar ta kori kamfanin Orano na Faransa

Tun a cikin shekarar 2015 Faransa ta haramta amfani da wannan sinadari, da ake amfani da shi wajen sarrafa robobin ruwan sha da sauran kayan zuwa abinci.