1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Faransa na son a kakaba takunkumai kan shugabannin Hamas

November 23, 2023

Faransa ta bayyana bukatar Tarayyar Turai ta kakaba wa jagororin kungiyar Hamas takunkumai, sakamakon harin da kungiyar ta kai Isra'ila wanda haddasa yaki a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4ZL6m
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron na FaransaHoto: Yves Herman/AP/picture alliance

Faransar na son Tarayyar ta Turai ta dora takunkuman a kan daidaikun jagoroin kungiyar Hamas ne, ganin a yanzu kungiyar ta EU ta tsaya ne kawai a kan matsayin Allah wadai a kan abin da kungiyar ta aikata.

A cewar sakatariyar harkokin ketaren faransa musamman kan al'amuran Tarayyar Turai, Laurence Boone, takunkuman za su shafi kudi ne kai tsaye musamman ma rufe asusunsu na bankuna.

Matakin kamar yadda Faransa da EU ke son yi, zai kuma shafi har da kawayen Hamas da kuma kungiyar Hizbollah, makamancin wanda aka dora wa jami'an kasar Iran da ke taimaka wa yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.