1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU na nuna damuwa kan halin da 'yan Gaza ke ciki

Abdullahi Tanko Bala MAB
October 27, 2023

A karshen taron kolin da suka gudanar, shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sun yi kiran samar da kafa ta kai kayan agaji a Zirin Gaza domin kaiwa ga Falasdinawa fararen hula da ke tsananin bukatar tallafi.

https://p.dw.com/p/4Y87n
Shugabannin kasashe da gwamnatoci sun halarci taro a birnin Brussels
Shugabannin kasashe da gwamnatoci sun halarci taro a birnin BrusselsHoto: Yves Herman/REUTERS

Wannan mataki a cewar sanarwar bayan taron zai bayar da damar kai taimakon jinkai da rarraba kayan agajin a Gaza. Shugabannin na EU sun bayyana matukar damuwa da halin tagayyara da jama'a suka shiga a Gaza. Kasashen na Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da a shigar da abinci da ruwa da magunguna da man fetur da kayan shimfida. Sun kuma ja hankali a tabbatar da cewa kayayyakin ba su fada hannun kungiyoyin ta'adda ba. Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai da Israila sun ayyana Hamas a matsayin yan ta'adda.

Karin bayani: Za a ci gaba da kai kayan agaji a Gaza

Taron ya yi amfani da kalmar tsahirtawa maimakon dakatar da bude wuta don samun kai kayan agajin. Jamus da Ostiriya sun ce amincewa da tsagaita wuta bai dace ba saboda hakkin da Israila ke da shi na kare kanta daga hare-haren Hamas. Sauran kasashe kamar Spain da Ireland da kuma Beljiyam sun goyi bayan tsagaita wuta saboda munin halin da jama'a ke ciki a yankin zirin Gaza.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na daga cikin wadanda suka ba da shawarwari
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na daga cikin wadanda suka ba da shawarwariHoto: Virginia Mayo/AP Photo/picture alliance

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi tsokaci kan shigar da kayan agajin yana mai cewa: " Mun yi la'akari da killacewa baki daya da hare-haren kan mai uwa da wabi da kuma gagarumin shirin farmaki ta kasa, cewa ba zai yiwu a iya ba da kariya ga al'umma fararen hula ba. Shi ya sa a waje guda muke kira a bayar da lokaci, don shirya kai hari kan 'yan ta'adda kuma wannan ba wai magana ce ta fatar baki ba, a shirye muke mu ba da gudunmawa."

Karin bayani: Sojojin Isra'ila sun kutsa Zirin Gaza ta kasa

A waje guda kuma, yawancin shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun ba da goyon baya ga ci-gaba da tallafa wa Ukraine da kudade a yakin da ta ke yi da Rasha. Sai dai kasashen Hangari da Slovakia sun nuna adawa gabanin taron na gaba da kungiyar za ta yi a watan Disamba kan batun. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana amannar cewa Kungiyar Tarayyar Turan za ta cimma masalaha na taimaka wa Ukraine duk da sabanin da ke tsakanin mambobin kasashen.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce EU za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce EU za ta ci gaba da tallafa wa UkraineHoto: Kenzo Tribouilliard/AFP

Olaf Scholz ya ce: " Mun tabbatar wa shugaban Ukraine ni da kaina a ganawar da na yi da shi a baya-bayan nan ta wayar tarho  cewa ba za mu sassauta ba a taimakon da muke yi wa Ukraine, kuma wannan babu ko gezau duk da sabuwar matsala mai daci da ta Sabbin sojojin Ukraine na horo mai hadaritaso na mummunan harin da Hamas ta kai wa Israila da ya hallaka fararen hula da dama."

Karin bayani:Sabbin sojojin Ukraine na horo mai hadari 

Ita ma yayin da take tsokaci, shugabar hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce kungiyar na aiki kan wani daftari na taimaka wa Ukraine domin ta sake gina kasarta bayan yaki. Von der Leyen ta ce: " Duk da matsalar da ta taso a Gabas ta Tsakiya, manufar da muka sa a gaba na taimaka wa Ukraine za ta ci gaba. Za mu ci gaba da ba da tallafin makamai da kayan aiki. Za mu ci gaba da bada dukkan tallafin kudi da ake bukata. A jimlance nahiyar Turai mun bada kusan Euro biliyan 83 na tallafin kudi ga Ukraine. Kuma a mataki na gaba za mu ba da karin Euro biliyan 50 ga kasar saboda Ukraine na bukatar tabbataccen tallafin kudi mai dorewa"

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da cewa za ta yi amfani da abin ta tara daga dukiyar da ta kwace daga hannun Rasha don taimaka  wa Ukraine wanda ya tasamma Euro biliyan 223.