1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Haramta abaya a makarantun Faransa

Mouhamadou Awal Balarabe AH
August 28, 2023

Ministan ilimin Faransa Gabriel Attal ya dauki matakin haramta sanya abaya a makarantun kasar domin kawo karshen cece-kuce kan wannan tufafi na gargajiya da ake alakantata da ta Islama.

https://p.dw.com/p/4VfLk
Hoto: Dominic Lipinski/dpa/picture alliance

Bangarorin siyasa na Faransa sun juma suna ka- ce-na-ce game da sanya abaya da  'yan matan Musulmi ke yi a makarantun kasar.  Hasali ma dai, dokar da aka amince da ita tun shekaru 19 da suka gabata, ta haramta amfani da duk wasu alamomi da ke fayyace addini dalibai kama a makarantun firamare har i zuwa kwalejoji da manyan makarantu. Amma dai majalisar Musulmi ta Faransa CFCM ta ce doguwar rigar da ke rufe jikin mace, ba ta danganta da addinin Musulunci, amma dai tsantsan al'ada ce. Sai dai tun a watan Nuwamba bara, ma'aikatar ilimi ta Faransa ta ambaci abaya da dogayen siket a matsayin tufafin da za a iya haramta wa dalibai idan suna sanya su domin nuna alamar addininsu. Shugabannin makarantu ne suka nuna damuwa kan karuwar amfani da dogayen riguna a azuzuwa, amma tsohon ministan ilimi ya yi burus da batun. Alkaluma sun nunar da cewar rikice-rikice da ke da nasaba da addini sun karu da 120% a makarantu tun bayan kisan gillar da aka yi wa malamin makaranta Samuel Paty a shekarar 2020. Sannan sanya alamomi da tufafi na addinai ya karu da fiye da kashi 150% a cikin shekarar da ta gabata.

Gwamnatin Faransa za tilasta yin amfani da dokar ga bako da dan kasa

Italien Ravenna | Symbolbild | Mädchen trägt Abaya Dress
Hoto: GoneWithTheWind/Imago Images

Ministan ilimi na Faransa Gabriel Attal ya jinjina wa darektotin makarantu kan kokarin da suke yi wajen kare manufar raba harkar ilimi da duk batutuwa da suka shafi addini, kuma ya yi alkawarin ganawa da su don fayyace musu yadda za su iya aiwatar da wannan doka ta haramta abaya. "Makarantarmu na fuskantar kalubale, kuma mun san da haka. A ‘yan watannin nan, an samu karuwar suka da ake wa tsarin iyakance addini da zamantakewar kasa, musamman sanya tufafin da ke da nasaba da addini irin su abaya ko kami da suka bayyana kuma suka samun gindin zama a wasu makarantu. Dole ne mu hada kai kuma mu bayyana karara cewa, abaya ba ta da gurbi a makarantunmu, da ma sauran alamomin addini." Sai dai ra'ayoyin sun sha bamban tsakanin 'yan siyasa na Faransa kan matakan haramta sanya a baya a makarantu. Shugaban jam'iyyar LR Eric Ciotti da ke bin tsarin jari hujja ya yi maraba da matakin hana sanya abaya a makaruntun Faransa, inda a shafinta na X (tsohon Twitter) ya ce sun sha yin kira da a dakatar da sanya abaya a makarantu. Sai dai a nata bangaren Clémentine Autain na jam'iyyar LFI da ke da matsakaicin ra'ayin gurguzu ta fusata da wadanda ta danganta da "'yan sandan tufafi", tana mai cewa haramta sanya abaya ya saba wa kundin tsarin mulkin Faransa, kuma ya yi hannun riga da ka'idodin bambance harkokin addini da na zamantakewar kasa. Ita ma Sophie Venetitay, mataimakiyar sakatare Janar na kungiyar malamai ta Faransa SNES-FSU ta yi kira da yi sara ana duba bakin gatari a kan matakin haramta abaya a makaratu  "Za mu mai da hankali sosai kan yadda shugabannin makaranta za su yi amfani da wannan doka ta haramta abaya. Dalili kuwa shi ne, idan kuna da matsayi mai tsauri a kan wannan batu, hadarin shi ne, dalibai za su kaurace wa tsarin ilimi na gwamnati domin su koma ga tsarin ilimin na addini. Dole ne a yi amfani da dokar 2004, amma dole ne a yi amfani da ita a cikin tattaunawa". Kashi 7% zuwa 10% na al'ummar kasar Faransa ne Musulmi. Amma kuma kalilan daga cikin 'ya'yansu mata ne ke amfani da abaya a makarantun kasar.