1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na son hana dalibai sanya abaya

August 28, 2023

Rahotanni daga Faransa na nuni da cewa, kasar za ta haramta wa dalibai sanya rigar abaya da wasu dalibai mata musulmai ke yi.

https://p.dw.com/p/4VdW7
 Abaya in Frankreich
Hoto: Nicolas Vallauri/MAXPPP/picture alliance

Ministan illimin Faransa Gabriel Attal ne ya sanar da hakan a wata hira a kafar talabijin din kasar. A cewarsa, bai kamata a iya tantance addinin dalibi ba da zarar ka shiga cikin aji.

Tuni dai hukumomi a kasar suka fara nuna maraba da wannan matakin da ministan ya sanar.

An dade ana tafka muhawara kan haramta wa dalibai sanya abaya a kasar. Sai dai kuma wata 'yar majalisa ta bangaren adawa, Clementine Autain ta zargi Faransa da kaurin suna wajen kin jinin musulmi da suka kai kimanin miliyan biyar a kasar.

A shekarar 2004 ne dai aka kafa dokar hana sanya kaya ko wani abu da zai nuna alamar addinin da mutum yake bi.