1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyun Najeriya sun fara yakin neman zabe

Uwais Abubakar Idris SB)(USU
September 28, 2022

Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin neman zabe na shugabancin Najeriya karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a birnin Abuja fadar gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/4HTyr
Nageriya PDP /  Ifeanyi Okowa /  Iyorchia Ayu / Atiku Abubakar
Ifeanyi Okowa / Iyorchia Ayu / Atiku AbubakarHoto: PDP/Facebook

A Najeriya ba da izinin fara yakin neman zaben da za'a yi a 2023 da hukumar zaben kasar ta yi ya sanya kara kankaman harkokin siyasa a kasar da alummarta suka dade da jiran wannan lokaci. Ko wadanne batutuwa ne ake sa ran za su mamaye yakin neman zaben a dai dai lokacin da alummar kasar ke matukar samun sauyi na tafiyara da kasar daga ‘yan siyasa?

Fagen siyasar dai tuni yake amo na  yakin neman zaben da ‘yan siyasa suka fara daga ranar Larabara nan inda suke alkawura na aiyyukan da za su yi wa jama'a don fitar masu da kitse a wuta daga hali na rayuwa da suke ciki. A tsari na yakin neman zabe dai kamata ya yi a mayar da hankali a kan batutuwa, amma aksin haka akan gani a Najeriya.

Karin Bayani:Tasirin addini a siyasar Najeriya

Kokari ne dai na kaiwa ga madafan iko ta hanyar neman  kuri'ar jama'a da tsarin dimukurdiya ya bayar bayan kowane shekaru hudu a Najeriya da dole sai an yi sauyin hannun mulki don a baje a faifai. Injiniya Buba Galadima sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa ta NNPP ya bayyana cewa suna fata kan samun nuna manufofi a yakin neman zaben da za a yi a shekara mai zuwa.

Hada hotuna | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar manyan 'yan takara na shugbancin Najeriya

Jam'iyyu 18 ne dai ke neman takara a zaben da za'a yi a shekara mai zuwa, kuma duk na kokuwar kai wa ga mukamin da yafi tsolewa kowa ido na neman zama shugaban kasa a Najeriya. Jamiyyar PDP ita ce jagaba a jerin wadanda ke adawa tare da kokarin karbe mulki daga hannun jam'iyyar APC da ke kan madafun iko.

A bisa dokar zabe dai akwai tsari da ka'ida da doka ta amince da ita domin yakin neman zabe kamar yadda Barrsiter Mainasara Umar masani a fanin shari'a ya bayyana. Manyan jam'iyyun Najeriya dai bas u kaiga kadammara da fara yakin neman zaben ba, domin daga APC zuwa PDP duk haka bagatatan suka dage kadammar da yakin neman zaben bisa dalilai mabambanta.