1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Kulla alakar samar da gas da EU

Muhammad Bello LM
October 2, 2024

A wani mataki da ke nuna karin matsa kaimin Kasashen Turai na ganin makamashin iskar gas ya wadace su sakamakon gibin da ke da alaka da yakin Rasha da Ukrain, EU ta sake shiga yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas din.

https://p.dw.com/p/4lM0q
Najeriya | Libiya | Tarayyar Turai | Iskar Gas | Bututu
Najeriyar dai na cikin kasashen da ke da dimbin arzikin man fetur da iskar gas a duniyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A yanzu dai tuni kasashen biyu wato Najeriyar da Libiya suka cimma matsayar tsara takardun yarjejeniya da ta hada da ta fasaha da kuma tattalin arziki, wanda za su amfane su kan shimfida bututun. An dai tsara za tura iskar gas din daga yankin Niger Delta a Najeriya zuwa Libiyan kafin su tike nahiyar Turan, aikin mai tsawon kilomita 5,600 da zai lashe biliyoyin daloli. Wannan na nuni da yadda nahiyar Turai ke dada kaimi wajen ganin kasashe masu arzikin makamashin iskar Gas kamar Najeriyar, sun goya mata baya kan kokarin cike gibin da yakin Rasha da Ukrain ya haifar. Bayanai dai na nuna cewar duk da sabata-juyatan siyasar kasar Libiya mai cike da tashe-tashen hankula, daga dukkan alamu nahiyar Turan a shirye take ta yi marhabin da duk wata kafa komai kankantarta da za ta kai ga samar da wadatuwar ta makamashin iskar gas a Turan Alkaluma dai sun tabbatar da cewar Najeriya a yanzu na da tilin arzikin danyan mai har ganga biliyan 37, kana akwai arzikin dimbin makamashin na iskar gas.