1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU ta ce manufofin FIFA ya ci karo da dokokinta

October 4, 2024

Kotun EU ta ce hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA bata da hurumin yin katsalandan kan musayar 'yan wasa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a Turai wanda hakan ya saba da dokokin shige da fice na tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/4lQQA
Tsohon 'dan wasan Paris Saint-Germain, Lassana Diarra a yayin taron hukumar kwallon kafar Faransa a 2023
Tsohon 'dan wasan Paris Saint-Germain, Lassana Diarra a yayin taron hukumar kwallon kafar Faransa a 2023 Hoto: BERTRAND GUAY/AFP/Getty Images

Gamayyar kungiyoyin 'yan wasa da ke nahiyar Turai sun yi na'am da wannan hukunci inda suka ce zai taimaka matuka wajen kare martabar 'yan wasan nahiyar a duk inda suka tsintsi kan su.

Karin bayani: FIFA: Kasashe uku za su dauki nauyin gasar 2030

Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da tsohon 'dan wasan Faransa da ya taka leda a kungiyoyi irin su Arsenal da PSG da Real Madrid, Lassana Diarra ya shigar na neman diyya daga FIFA da kuma kungiyar kwallon kafa ta Belgium biyo bayan kwantaragin da ya soke da kungiyar Lokomotiv ta Rasha a 2014. Diarra ya bukaci FIFA da ta biya shi diyya sakamakon rasa damar taka leda da yayi da Rasha sakamakon dokokin FIFA.