SiyasaTurai
EU ta ce manufofin FIFA ya ci karo da dokokinta
October 4, 2024Talla
Gamayyar kungiyoyin 'yan wasa da ke nahiyar Turai sun yi na'am da wannan hukunci inda suka ce zai taimaka matuka wajen kare martabar 'yan wasan nahiyar a duk inda suka tsintsi kan su.
Karin bayani: FIFA: Kasashe uku za su dauki nauyin gasar 2030
Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da tsohon 'dan wasan Faransa da ya taka leda a kungiyoyi irin su Arsenal da PSG da Real Madrid, Lassana Diarra ya shigar na neman diyya daga FIFA da kuma kungiyar kwallon kafa ta Belgium biyo bayan kwantaragin da ya soke da kungiyar Lokomotiv ta Rasha a 2014. Diarra ya bukaci FIFA da ta biya shi diyya sakamakon rasa damar taka leda da yayi da Rasha sakamakon dokokin FIFA.