1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Emirates zai dakatar da aiki a Najeriya

Ramatu Garba Baba
August 18, 2022

Kamfanin jiragen sama na Emirates na Hadaddiyar Daula Larabawa mai mazauni a birnin Dubai ya sanar da dakatar da aikin jigila daga Najeriya daga watan Satumba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/4Fj2o
Airbus A380 | Emirates Airlines
Hoto: Daniel Kubirski/picture alliance

Kamfanin jiragen sama na Emirates na Hadaddiyar Daula Larabawa da ke da mazauni a birnin Dubai ya sanar da cewa, zai dakatar da aikin jigilar fasinja daga Najeriya kama daga watan Satumba mai zuwa. A cikin sanarwar kamfanin ya ce, ya  dauki matakin ne don yadda ya kasa fitar da kudadensa daga kasar da kuma rage yawan asarar da ya ke tafkawa a sakamakon matsaloli masu nasaba da faduwar darajar naira a kasuwannin duniya, tun bayan da gwamnatin Najeriyar ta dage kan sai an siyi tikitin jirgin Emirates da takardar kudin naira. 

Tun daga watan Agustan 2021 gwamnatin Najeriyar ta hana yin hada-hadar canjin kudaden waje a kasar baya ga dalar Amirka, lamarin da ya haifar da nakassu ga kananan 'yan kasuwa da masu zuba jari. Dubai na daya daga cikin biranen da 'yan kasuwar Najeriya dama masu son shakatawa ke yawan zuwa.