1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Dubban mazauna Gaza sun kwashe abincin agaji

October 29, 2023

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinu, ta ce dubban mazauna Zirin Gaza sun kwashe kayayyakin abincin da aka ajiye domin rarrabawa.

https://p.dw.com/p/4YAvx
Yadda mazauna Gaza suka yi wawason abinci
Yadda mazauna Gaza suka yi wawason abinciHoto: Mohammed Abel/AFP

Jagoran hukumar, Thomas White wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, ya ce kutsen da mutanen suka yi wani tabbaci ne cewa doka ta soma tabarbarewa a yankin.

Isra'ila dai ta sanar da yi wa Zirin Gaza kawanya da kaddamar da luguden wuta ne bayan harin da kungiyar Hamas ta kai kasar a ranar bakwai ga wannan wata na Oktoba.

Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya dai sun kara kira a yau Lahadi game da matsanancin taimakon jinkai da ke a yankin na Gaza inda Isra'ila ke tsananta hare-hare ta sama da ma kasa.

Wannan kuwa na zuwa ne yayin da hukumar asibitin Al Quds ke cewa dakarun Isra'ila ta ba su umurnin kaurar da daruruwan marasa lafiya da ma'aikata daga arewacin Gazar zuwa kudancin zirin.