1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan mutane sun mutu a rikicin Isra'ila

October 8, 2023

Alkalumma sun yi nuni da cewa, an kashe mutane kimanin 700 yayin da wasu dubu biyu suka jikkata a rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/4XGpW
Yadda hare-hare tsakanin Isra'ila da kuma Hamas ya lalata gine-gine
Yadda hare-hare tsakanin Isra'ila da kuma Hamas ya lalata gine-gineHoto: Andrei Shirokov/Tass/IMAGO

Alkalumma na zuwa ne kwana guda tun bayan barkewar rikici tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hamas da ke zirin Gaza. A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, offishin yada labarai na gwamnatin Isra'ila ya kuma ce an yi garkuwa da wasu mutane sama da 200. Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa, ana tsare da 'yan Isra'ila kimanin 170 a zirin Gaza.

Karin bayani: Mutane da dama sun halaka a Isra'ila da Zirin Gaza

A gefe guda, gwamnatin Nepal ta nuna damuwarta kan batan wasu dalibai 11 'yan asalin kasar a rikicin. Ministan harkokin wajen kasar ya ce daliban 11 da suka yi batan dabo na karatu ne a kwalejin ayyukan gona da ke Kibbutz Alumin a kusa da iyakar Gaza.

Karin bayani: Duniya na Allah wadai da sabon rikicin Hamas da Isra'ila

Daliban dai na daga cikin dalibai 17 'yan asalin Nepal da ke karatu a kwalejin. An ruwaito cewa wasu hudu daga cikinsu sun jikkata yayin da aka tabbatar da lafiyar mutum biyu.