1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dandalin Matasa: 23.11.2023

November 30, 2023

Masana'antar Kannywood da masu sha'awar fina-finai da wakokin Hausa na ci gaba da jimamin rasuwar daya daga cikin fitatun daraktoci kana jarumi Aminu S Bono.

https://p.dw.com/p/4Zcbp
Hoto: Isa Bawa Doro/CEO Kannywood exclusive multimedia

Hausawa ke cewa '' mutuwa rigar kowa'' a ranar Litinin 20 ga watan Novemba 2023 ne kwatsam aka samu labarin rasuwar Aminu S Bono daya daga cikin daraktoci a masana'antar Kannywood. Muturwar daraktan ta girgiza wannan masana'antar Fina-finai da wakoki ta Arewacin Najeriya da ma masoyanta.Shirin Dandalin Matasa ya duba rayuwar marigayin. Daga kasa za a iya sauran sautin shirin.