1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Siriya ya kubuta daga masu garkuwa a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
May 23, 2018

An kama Abdul Nasir a ranar 16 ga watan Mayu a kan hanyarsa ta zuwa wajen gina hanyoyi a babban birnin Sokoto, an kuma kashe 'yan sanda uku da suka yi kokari na kubutar da injiniyan.

https://p.dw.com/p/2yD5h
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Injiniyan dan asalin kasar Siriya da aka yi garkuwa da shi a Najeriya a makon da ya gabata ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane da ya fada hannunsu a jihar Sokoto Arewa maso Yammacin Najeriya kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Abdul Nasir an kama shi a ranar 16 ga watan Mayu a kan hanyarsa ta zuwa wajen gina hanyoyi a babban birnin Sokoto an kuma kashe 'yan sanda uku da suka yi kokari na kubutar da injiniyan dan asalin Siriya.

A cewar Cordelia Nwawe me magana da yawun 'yan sanda da misalin karfe 12:30 ne na daren Talatar masu garkuwan suka saki Abdul Nasir a kan hanyar Arkilla da ke wajen birnin na Sokoto. Sai dai Nwawe ba ta yi karin haske ba ko an biya kudin fansa. Kama mutane don neman kudin fansa dai na kara samun gindin zama a yankin na Arewa maso Yammacin Najeriya.