1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwar kungiyoyi kan tsaro yayin zabe

Uwais Abubakar Idris
March 16, 2023

A Najeriya kungiyoyin farar hula masu sa ido a kan zabubbukan kasar sun bayyana damuwa kan yiwuwar fuskantar matsalolin rashin tsaro a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki a kasar.

https://p.dw.com/p/4Onaj
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kungiyoyin sun bayyana halin da ake ciki a game da shirin hukumar zabe mai zaman kanta game da zaben da za a yi na gwamnoni da ‘yan majlisun dokokin jihohi a ranar 18 ga wannan watan na Maris. Sun duba ko hukumar zaben ta shirya musamman batun ake wa da sakamakon zabe ta yanar gizo da ma na'urar tantance masu zabe Bvas. Wani batun da kungiyoyin suka yi nazari a kai shi ne zaman tankiya a wasu jihohi da zai iya haifar da hatsaniya a lokacin zaben. Ko me suka hango ya zuwa yanzu? Zaliha Lawal jami'a ce a kungiyar Connected Development da suke amfani da manhajar Uzabe wajen sa ido a kan zaben na Najeriya.

Aikin zabe a Najeriya
Hoto: IMAGO/NurPhoto

Ta ce yanayin zaman tankiya da ake fuskanta a jihohi da dama da za'a yi zaben ya sanya nuna damuwa. A jihohin Kano da Rivers da Lagos da dai sauransu ana cikin zaman dar dar. Mallam Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar Cislac ya bayyana abinda ke daga masu hankali.

Fuskantar koma baya na yawan mutanen da suka yi zabe a wannan lokaci musamman zaben shugaban kasa inda suka gano cewa kashi 27 kacal na masu jefa kuri'ar suka fito zabe abin damuwa ne a kasa da ke da masu zabe sama da milyan 90. To sai dai irin yadda zaben shugaban Najeriya ya kasance ya jawo martani daga al'umma musamman matasa. To sai dai ga Hamzat Lawal shugaban kungiyar Code yace bai kamata wannan ya sanya ja da baya ba.

Aikin zabe a Najeriya
Hoto: Sunday Alamba/AP/dpa

Amma ga Malama Zaliha Lawal ta bayyana abin da ke daga masu hankali a game da batun tsaro a zaben gwamnonin da ‘yan majalisun dokoki na jihohi.

A yanzu dai ‘yan Najeriya da ma sauran kungiyoyin da ke sa ido a kan zabe sun sa ido ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar bisa alkawurran da ta yi musamman aika da naurar Bvas da kuma aikewa da sakamakon zaben ta yanar gizo wanda zai baiwa zaben sahihanci da karbuwa.