1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Muhawara kan yaki da cin hanci

Ahmed Salisu
May 24, 2018

Takadddama ta kaure kan kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cewar tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo bai yi wani abin kirki ba dangane da gyara wutar lantarki a kasar duk da yawan kudaden da ya kashe

https://p.dw.com/p/2yGt9

A 'yan kwanakin da suka gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamantin Obasanjo b ta tabuka wani abin kiriki kan gyaran wutar lantarki ba a kasar duk kuwa da cewar an batar da biliyoyin daloli kan wannan batu. Kalaman nasa sun haifar da zazzafar muhawara a kasar inda wasu ke cewar ba su kai zuci yayin da wasu ke cewar ya yi hakan ne saboda kishin kasar da ya ke yi da kuma yunkurinsa na magance cin hanci da rashawa.