1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambaruwar majalisa kan tsarin zaben Najeriya

Uwais Abubakar Idris
April 19, 2018

A Najeriya majalisar dokokin kasar ta yi watsi da batun sauya tsarin gudanar da zabubbuka da ta dage a kai, abin da ya haifar da takaddama bayan da shugaban kasar ya ki sanya hannu a kanta.

https://p.dw.com/p/2wLzL
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Watsi da dagewa a kan sauya jadawalin zaben Najeriyar dai abu ne da ya kawo ja-in-ja da ma kai ruwa ranar da aka fuskanta a kan wannan batu. Domin tun daga lokacin da majalisun suka sauya tsarin da nufin a fara gudanar da zabensu sannan a yi na shugaban kasa a karshe, an dai kai ruwa rana da ma raba majalisar gida biyu a tsakanin masu goyon baya da masu adawa. Ko me suka hango a yanzu suka yi watsi da daukacin lamarin. Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na cikin wadanda suka yi muhawara tare da amincewa da komawa tsarin da ake da shi.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Ranakun zabe na shugaban kasa da 'yan majalisa sun bambanta a NajeriyaHoto: DW/Gänsler

A bisa tsarin da aka amince da shi tare da tura shi zuwa ga kwamitocin majalisun biyu, an tsara za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, sannan sai a yi na gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki. Bisa wannan tsari za'a yi zabubbuka biyu maimakon guda uku da suka so a yi. Wannan ya sanya Hon Sidi Yakubu Karasuwa na majalisar wakilan Najeriyar bayyana muhimmancin wannan ga demokradiyyar Najeriya. Tun kafin wannan mataki shugaban Najeriya ya ki sanya hannu a sauya tsarin da aka yi, a yayin da ake muhawarar halacci da ikon yin haka ga majalisar, domin hukumar zaben kasar ta dage kan cewa ita ce ke da ikon sanya tsari da ranakun zabe.